Gwamnatin Jihar Kano ta zata horas da Malaman makaranta kimamin 600 wanda yanzu haka aka dauke su a ma’aikatu da kuma hukumomi daban-daban.
Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Sanusi Saidu Kiru ya sawa hannu, ta ofishin jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimin jihar.
Kwamishin ilimin jihar yace za’a horas da malaman ne a matsayin su na sabbi a fannin aikin koyarwa, kuma ya yabawa gwamnatin jihar bisa daukar nauyin horas da sabbin malaman makarantar.
Ya kuma bayyana cewa wannan wani yunkuri na gwamnatin jihar domin bunkasa ilimi a jihar.