Gwamnatin jihar Kano tace tana shirin ciyar da mutane miliyan 4 a cikin wannan watan na Azumi a fadin kananan hakumomi 44 dake jihar.
Kwamashinan yada labarai da harkokin cikin gida a ganawar sa da manema labarai a jiya, ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta ware naira biliyan 6 domin shirin ciyar da talakawa da mabukata a jihar.
Kwamashinan yayi bayanin cewa, Birnin Kano mai yawan al’umma, dake da kananan hakumomi 8 za’a samar da cibiyoyin buda baki na musamman guda 90, a masallatai, guraren taruwar jama’a, makarantun Tsangaya, asibitoci da islamiyyu domin ciyar da mutane dubu 18 a kowace rana. Yace kasafin kudaden da aka ware za’a sayi kayayyakin abinci, da hayar tukwane da kuma kudaden alawus-alawus ga masu dahuwa da jami’an tsaro, tare da sayen itacen girki da sauran kayayyaki har zuwa karashen watan na Ramadana.