Kotu ta umurci Binance da ya bai wa EFCC bayanan duka masu hada-hadar kudade ta shafin a Najeriya

0 104

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umurci Kamfanin hada-hadar kudi Binance da ya bai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Cikakkun bayanai kan duka mutanen da suke hada-hadar kudade ta shafin.

Kotun ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan karar da hukumar EFCC ta shigar na neman bayanai kan ‘yan Najeriya da ke ciniki a shafin Binance.

Hakumar EFCC ce ta gabatar da karar tana mai dogaro da sassa na 6 (b), (h), (I), 7 (1), (a) (2), da 38 na dokar laifukan Tattalin Arziki da Kudade ta 2004 da Sashe na 15 na Dokar yaki da almundahanar Kuɗade ta 2022 wacce aka yiwa gyaran fuska.

A cikin takardar amincewa da bukatar wani jami’in hukumar EFCC, Hamma Bello, ya bayyana cewa, tawagar bincike ta musamman dake zaune a ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ta samu bayanan sirrin cewa an yi ta’ammali da kudade ta hanyar da bata dace ba, tare da halarta kudaden haramun da kuma tallafawa ayyukan ta’addanci. A baya dai hakumar ta tsare wasu jami’an kamfanin guda biyu kan ayyukan shafin na yanar gizo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: