Kungiyar kwadago tana goyon bayan yajin aikin da kungiyoyin ma’aikatan jami’a ke yi

0 107

Kungiyar kwadago ta kasa NLC tace tana goyon bayan yajin aikin da kungiyar ma’aikatan jami’a NASU da SSANU ke gudanarwa, tana mai kira da a gaggauta biyan albashin ma’aikatan da aka rike.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Joe Ajaero, tace babu wani dalili ko bayani da zai sa a rike albashin ma’aikatan tun farko.

Ajaero yace rike albashin ma’aikatan ya jefa su cikin matsainaicin halin kunci da damuwa.

Kungiyar NLC tayi kira ga gwamnati da ta gaggauta biyan albashin, tana mai shawartar ta da kada tayi wasa da hankalin kungiyar.

A jiya ne dai, kungiyoyin suka tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 7 a fadin kasa. Membobin kungiyoyin sun rufe harkoki a jami’oi bisa umarnin uwar kungiya ta kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: