Tsananin zafi yasa an rufe daukacin makarantun dake kasar Sudan ta kudu

0 261

An rufe daukacin makarantu a Sudan ta Kudu, sakamakon tsananin zafin da kasar ke fama da shi cikin makonni biyu.

Ma’aikatar lafiya da ilimi sun bai wa iyaye shawarar kar su bari ƴaƴansu su fita, sakamakon hasashen tsananin zafin ka iya kai wa maki 45 a ma’aunin selshiyos.

Ma’aikatun sun ce, ana bibiyar yanayin sau da ƙafa, sai dai babu ranar buɗe makarantun.

Sun ce duk makarantar da aka samu a buɗe, za ta rasa lasisinta, kamar yadda hukumomin suka yi gargaɗi. A makon da ya gabata ne, aka ba da rahoton mutuwar kimanin yara 15 sakamakon sanƙarau da wasu cututtukan da zafi ke haddasawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: