Gwamnatin jihar Zamfara ta karbi ‘yan mata hudu da ‘yan ta’adda suka sace a watan Janairu

0 246

Gwamnatin jihar Zamfara ta karbi ‘yan mata hudu da ‘yan ta’adda suka sace a watan Janairu bayan da masu garkuwa da su suka sake su.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa ‘yan matan sun hada da ‘yar shekarar ajin karshe a kwalejin fasaha da kimiyya ta jihar Zamfara, ZACAS, Ummulkhairi Musa da kuma Jamila Isa, da Aisha Isa, da kuma UmmulKhairi Umar.

An sace su ne a lokacin da suke dawowa daga daurin aure a hanyar Kaura Namoda zuwa Birnin Magaji a ranar 15 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da Sulaiman idris, mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal ya fitar, ya ce an kubutar da ‘yan matan ne ta hannun gwamnati.

A cewarsa, gwamnan ya shiga damuwa bayan da ya ga bidiyon ‘yan matan da aka sace suna rokon iyalansu da gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ‘yan matan za su koma wajen iyayen su daga zarar an kammala duba lafiyar su. Da take zantawa da manema labarai, da ya daga cikin wadanda aka ceto Umulkhairu Musa, ta bayyana godiya ga Allah da wadanda suka tsaya musu a lokacin da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: