Sanatoci sun gargadi shugaban kasa Bola Tinubu bisa yunkurin yin amfani da soji wajen magance rikicin jamhuriyyar Nijar

0 251

Sanatocin Arewacin kasarnan a Majalisar dattawa, sun gargadi Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yin amfani da karfin soji wajen magance rikicin kasar Nijar.

Kakakin kungiyar Sanatocin Arewa Sanata Suleiman Sumaila ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Kungiyar Sanatocin ta bukaci shugaban kasar da ya yi amfani da hanyoyin siyasa da diflomasiyya don maido da mulkin dimokradiyya a Nijar.

A cewar kungiyar Sanatocin Arewan, tsoma bakin sojoji a Nijar zai iya haifar da matsaloli a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno.

Idan za a iya tunawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta yanke huldar diflomasiyya da Najeriya bayan da wakilan ECOWAS da ta aika zuwa kasar sun kasa cimma matsaya da sojojin.

A watan da ya gabata ne, gwamnatin mulkin soji ta hambarar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.

Kuma kawo yanzu ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin yammacin Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: