Gwamnatin Kano ta karyata zargin karbo bashin dalar Amurka miliyan 6.6

0 119

Hukumar kula da basussuka ta jihar Kano ta karyata zargin da wata kungiya a APC ta yi cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta karbo bashin waje na dala miliyan 6.6 cikin shekaru biyu.

Kungiyar APC Patriotic Volunteers, karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji, ta ce tana da rahoton da ke nuna cewa an karbo bashin daga ofishin kula da basussuka na kasa.

Sai dai darakta janar na hukumar basussuka ta Kano, Hamisu Sadi-Ali, ya ce gwamnatin yanzu ba ta kulla ko rattaba hannu kan kowanne sabon bashi na cikin gida ko na waje ba tun daga hawanta mulki. Ya kalubalanci kungiyar APC da ta fitar da hujjoji a bainar jama’a daga hukumar DMO da ke tabbatar da gwamnatin jihar ta karbi bashin da ake zargi, yana mai cewa zargin Ganduje na nuna rashin fahimta ko wata bukata ta siyasa kawai.

Leave a Reply