Rundunar ‘Yan sanda a Jigawa ta kama mutane 14 tare da kwato haramtattun kudade a wani samame da ta kaddamar

0 254

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta samu nasara bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai a kauyen Digawa da ke karamar hukumar Birnin Kudu, inda aka kama mutane 14 da wasu kayayyakin da ake zargi.

Samamen ya biyo bayan wani harin da masu damfara daga Digawa suka kai kauyen Dumus a ranar 11 ga Yuni, wanda ya yi sanadin mutuwar Isma’il Ibrahim mai shekara 60, da jikkata mutane takwas.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya ce aikin ya gudana ne a ranar 12 ga Yuni, ranar dimokuradiyya, kuma ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan wata kungiyar masu aikata laifuka. Ya ce ana ci gaba da bincike kan wadanda ake zargi yayin da ake shirin gurfanar da su gaban kotu bayan kammala binciken da ake gudanarwa.

Leave a Reply