Rundunar ‘Yan Sanda ta kama wani matashi a jihar Bauchi bisa zargin satar bayanan mutane ta yanar gizo

0 500

Rundunar ‘Ƴan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane.

An kama Ya’u, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara.

Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane.

Kakakin rundunar Jihar CSP Ahmed Wakil,, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki.

Daga baya, bincike ya gano cewa ana amfani da sunayen Hansatu Ya’u da Umar Ya’u wajen karbar kuɗin jama’a a yanar gizo. Bayan ƙorafin da aka samu, Kwamishinan ’Yan sanda ya umarci gudanar da bincike na fasaha wanda ya kai ga kama Ya’u a ranar 5 ga Yuni, 2025. An kwato kati tara na ATM, katin zabe, na’urar MiFi, da sauran kayayyakin da suka tabbatar da laifin. Ya’u ya amsa cewa ya damfari mutane kusan 40 cikin shekaru biyar. An miƙa shi zuwa Rundunar ’Yansandan Kano don ci gaba da bincike da shari’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.