Gwamnatin mu ba zata juyawa Pantami baya ba

0 76

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatin san a tare da ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami wanda ke cigaba da fuskantar suka daga wasu yan kasar kan kalaman da yayi a shekarun baya dangane da kungiyar Taliban da Al Qaeda.

A sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar mai dauke da sanya hannun Garba Shehu shugaban yace an samu wani sabon salon yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula yarfe dangane da kalamun da suka yi a baya koda sun yi watsi da su.

Sanarwar tace irin wannan yarfe kan shafi rayuwa da harkokin irin wadannan mutane ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.

Fadar shugaban kasar tace irin wannan yarfen aka kaddamar akan ministan sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim Pantami daga masu neman ganin an raba shi da mukamin sa, ba tare da la’akari da matsayin sa kan kalamun da ake zargin yayi ba shekaru 20 da suka gabata.

Sanarwar tace tuni ministan ya nemi gafara kan kalamun da yayi a baya wadanda akayi su a shekara ta 2000 lokacin yana sama da shekaru 20 kuma lokaci ya sauya yadda yanzu ya kama hanyar cika shekaru 50 a shekara mai zuwa.

Sanarwar ta kara da cewar yan Najeriya masu hankali sun fahimci cewar matakin da aka dauka kan ministan basu da nasaba da kalamun sa, sai dai matakan da yake dauka na kawo sauyi a bangaren sadarwa da kuma tabbatar da rajistar duk masu dauke da lauyukan waya wajen ganin sun samu lambar dan kasa.

Sanawar tace bayanan da aka samu na nuna cewar wasu editocin kafofin yada labarai sun ki karbar makudan kudade domin kaddamar da kamfe domin bata sunan ministan, abinda ke nuna cewar dama shiri akayi akai kuma gwamnati ta kaddamar da bincike akai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: