Yar Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta biyu Aishatu Ahmadu Bello ta mutu tana da shekara 75.

Marigayiyar tsohuwar matar Marafan Sokoto ce Alhaji Ahmad Danbaba.

Jaridar DailyNagerian ta ruwaito cewa Hassan Dan baba ne ya tabbatar da mutuwar mahaifiyar ta sa a ranar Juma’a, yana cewa ta mutu a wani asibiti ne a Dubai bayan fama da wata matsagaiciyar rashin lafiya.

Hassan ya ce ana shirye-shiryen yadda za a dawo da ita Najeriya ne daga Dubai domin a binneta a Sokoto.

Mahaifinta Sir Ahmadu Bello shi ne Premier arewa na farko kuma na karshe wanda ya rike mukamin daga shekarar 1954 zuwa 1966 lokacin da aka kashe shi a wani juyin mulkin soji.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: