Gwamnatin Najeriya tana aiki domin kara yawan jami’an tsaro a ƙasar – Sen Yar’adua

0 163

Sanata Abdulaziz Yar’adua ya ce gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki domin kara yawan jami’an tsaro domin ƙara murƙushe ayyukan miyagu da ke ƙaruwa a ƙasar.

Najeriya dai na fama da ayyukan ƴanbindiga da sace-sacen jama’a da kuma satar mai da sauran laifuka.

Sanata Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya ya koka kan adadin jami’an tsaron da ke Najeriya wanda a jumulla ba su kai ko miliyan ɗaya ba a ƙasar da ke da yawan mutum miliyan 220.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels inda ya ce gwamnati tana ƙoƙari domin gyara hakan. A cewarsa, baya ga rashin isassun jami’an tsaro, rashin ci gaba shi me wani abu ne da ke janyo ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: