Gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba

0 119

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba, yana mai cewa wasu kasashen Afirka da suka hada da Guinea, da Togo, da Mali na biyan kudin wutar lantarki fiye da ‘yan Najeriya.

Adelabu, yayin ziyarar da ya kai hedkwatar kamfanin wutar lantarki na Ikeja da ke jihar Legas a ranar Alhamis, ya ce yan Najeriya za su kasance a shirye su biya karin kudi idan sun samu isasshiyar wutar lantarki.

Ministan ya kuma bayyana cewa kalubalen da ake fuskanta a fannin wutar lantarki ba zai yuwu ba idan har masu ruwa da tsaki basu bada gudunmuwar su yadda ya kamata.

Ya nuna damuwarsa cewa da yawa daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 ba su shirya zuba jari a ayyukan samar da wutar lantarki ba, inda ya bayyana gwamnati za ta magance hakan ta hanyar kafa dokar da za ta ba da damar zuba jari a matsayin abin da ya dace ga dukkan kamfanonin. Ministan ya kuma kara da cewa ‘yan Najeriya na nuna damuwarsu kan rashin wutar lantarki da ake samu a halin yanzu musamman ganin yadda ake samun karin bukatu saboda shigowar yanayin zafi da kuma rashin man fetur bayan cire tallafin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: