Gwamna Namadi ya nemi bankin duniya da ya fadada tallafin da yake bawa jihar

0 154

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yi kira ga bankin duniya da ya fadada tallafin da yake bai wa jihar a fannin sauye-sauye na zamani, da dabarun tattalin arziki na zamani da kawar da fatara da shugabanci na gari domin samun ci gaba mai dorewa.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin daraktan bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri a fadar gwamnati dake Dutse.

Gwamna Namadi ya bukaci Daraktan da yayi amfani da ziyarar a wani sabon salo na bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa wajen tallafawa harkokin sadarwa na zamani da dabarun tattalin arziki na zamani don bunkasar ci gaban jihar nan.

Gwamna Namadi ya kuma koka kan yadda yara ba sa zuwa makaranta, da ambaliyar ruwa da sauran munanan illolin da sauyin yanayi ke haifarwa wanda ya ce akwai bukatar a hada kai don magance su. Daga nan Malam Umar Namadi ya ba da tabbacin aniyar gwamnatinsa na hada kai da bankin duniya wajen aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa domin tunkarar kalubalen da ke akwai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: