Sojojin Nijeriya sun ci alwashin kuɓutar da ɗaliban makarantar Kuriga

0 288

Rundunar sojin Najeriya ta yi alƙawarin kuɓutar da fiye da ɗalibai 200 da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja game da ayyukan rundunar sojin a makonni biyu da suka gabata, Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin a shirye suke su ceto ɗaliban ba tare da an rasa rai ba.

Ya kuma ɗora laifin sace ƴangudun hijira a kwanakin da suka gabata daga Gamboru-Ngala a jihar Borno kan rashin mutunta umarni inda suka fita daga sansanin domin neman itacen girki ba tare da sanar da jami’ai ba. Tun dai bayan sace ɗaliban ne, shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gano ƴanbindigar tare da kuɓutar da ɗaliban inda ya nanata cewa gwamnati ba za ta biya kuɗin fansa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: