Majalisar dattawa ta musanta rahotannin dake cewa zatayi bincike a matatun man kasar nan

0 254

Majalisar dattawa ta kasa ta yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin cewa za ta bankado duk wani ba daidai ba dake da alaka da kwangila a ayyukan gyaran matatun man kasar nan.

Kwanan nan, wani rahoto ya yi ikirarin cewa majalisar dattawa ta hannun kwamitinta na wucin gadi kan binciken da ake yi a matatun man kasar nan, ya sha alwashin bankado duk wata badakala dake da alaka da kwangila da gudanar da aikin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin Mai na kasa Olufemi Soneye ya rabawa manema labarai. Shugaban kwamitin wucin gadi, Sanata Ifeanyi Ubah, ya nuna rashin jin dadinsa da wannan rahoton, inda ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar nan, ba za ta iya yanke hukunci kan batun da har yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: