Gwamnatin shugaba Tinubu ta baiwa mata dama domin suma su bada tasu gudunmawar

0 221

Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu, tace wannan gwamnatin ta shugaba Bola Ahmed Tinubu ta baiwa mata dama domin suma su bada tasu gudunmawar domin cigaban kasa.

A cewar ta, gwamnati tana kokari domin daid-daita Najeriya da kuma magance matsalolin da mata ke fuskanta a kasar nan.

Matar shugaban kasar ta bayyana haka ne yayinda ta karbi bakuncin karamar Ministar Yan sanda Imaan Sulaiman-Ibrahim, wacce ta jagoranci tawagar manyan jami’an yan sanda mata zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja.

Oluremi Tinubu, ta bukaci tawagar jami’an yan sandan mata dasu magance wasu matsaloli ciki harda fyade,cin zarafin yara da safarar mutane da kuma cin zarafin yaya mata.

Ta kuma kara da cewa tana jiran lokacin da za’a samu macen da zata zama Babbar Sufeton yan sanda ta kasa.

Karamar Ministar yan sandan Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa dai-daiton jinsi, da kare hakkin mata da kuma samar da damar-makin cigaba ga mata shine babban abinda ke kawo cigaban al’umma. Imaan Sulaiman-Ibrahim, itace mace ta farko da shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu ya nada a matsayin karamar Ministan yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: