Ma’aikatar lafiya a Falasdinu tace adadin wadanda suka mutu a zirin Gaza ya karu zuwa mutane 700.
Hukumomin lafiya sun ce yara 100 da mata 100 yanzu haka harin makamin Isra’ila ya kashe.
a jiya samu mutuwar mutane da ba’a taba gani ba, inda mutane sama da 300 suka mutu a lokaci guda.
Hukumar lafiya a kasar tace biyu cikin uku na wadanda suka mutu fararan hula ne.
Wani mumman hari yayi sanadiyar mutane na barin gidajen su domin neman mafaka. A wani hari da aka kai wanda ya fada wani gida ya kashe mutanen dake kan titina da wadanda ke cikin gida.