Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na saka yara miliyan 15 da ba sa zuwa makaranta Aji

0 149

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na mayar da yara miliyan 15 da ba sa zuwa makaranta  Aji nan da shekarar 2027.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman shine ya bayyana hakan jiya a Abuja.

Mamman ya bayyana cewa matsalar ta kasance wani babban al’amari wanda acewarsa mummunar illa ce rashin zuwa makaranta, don haka dole ne a dauki matakin magance matsalar da muhimmanci.

Ya ce samar da tsare-tsare bai kai a tunkari kalubalen ba amma aiwatar da manufofi masu kyau zasu taimaka matuka wajen magance matsalolin yaran da ba su zuwa makaranta. Ministan ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sake dawowa da shirin  ciyar da daliban makarantu a matakin farko domin bunkasa harkar ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: