Shugaba Tinubu zai halarci gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 38 a garin Damaturu

0 216

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku da Gwamnonin jihohin Borno da Yobe na daga cikin manyan baki da ake sa ran za su halarci gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 38 a garin Damaturu na jihar Yobe.

Kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida, yada labarai da al’adu, Abdullahi Bego shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu da ke Damaturu, babban birnin jihar.

Ya ce taron wanda za a fara a yau juma’a, a ranar 27 ga watan Disamba, zai samu halartar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin babban bako na musamman, yayin da Gwamna Zulum zai kasance shugaban rufe taron.

Ya kara da cewa mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, zai kasance babban bako na musamman, yayin da ministan harkokin ‘yan sanda, Sanata Ibrahim Geidam, zai kasance shugaban bikin bude taron.

A cewar Bego, kimanin masu shiga gasar 296 ne za su fito daga jihohi 36 na kasar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja a cikin rukunoni 10 na gasar. Ya ce Yobe tana da ‘yan takara takwas a gasar kuma bisa irin goyon baya da horo da suka samu, jihar na da kwarin gwiwar cewa za su yi nasara yayin wannan gasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: