Majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar yin kwaskwarima ga dokar kasafin kudi na 2023

0 242

Majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar yin kwaskwarima ga dokar kasafin kudi na 2023 don tsawaita aiwatarwa daga ranar 31 ga Disamba 2023 zuwa 31 ga Maris 2024.

Majalisar ta kuma zartar da wani kudiri na yin kwaskwarima ga dokar karin kasafin kudi na 2023 don tsawaita aiwatarwa daga 31 ga Disamba 2023 zuwa 31 ga Maris 2024.

An dauki wannan mataki ne yayin zaman majalisar da aka yi jiya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja.

Haka nan majalisar ta amince da nadin daya daga cikin sabbin alkalan da aka tabbatar da nadinsu mai shari’a Haruna Tsammani daga yankin Arewa-maso-Gabas, wanda ya jagoranci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a 2023. Majalisar ta tabbatar da su ne bayan wata muhawara da ‘yan majalisar suka yi kan kasafin kudin bangaren shari’a tare da bayyana rashin dacewar barin kujeru a kotun koli na tsawon lokaci ba tare da nada mukamai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: