Gwamnatin tarayya ta cigaba da biyan wadanda suka ci gajiyar shirin N-Power a kasar nan

0 111

Wadanda suka ci gajiyar shirin na jiran a biya su albashinsu na wasu watanni daga gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu, ta ce za a ci gaba da biyan bashin wadanda suka ci gajiyar shirin wanda tuni aka fara  tun daga ranar Laraba.

Edu ta bayyana hakan ne yayin hira da ita cikin shirin siyasa na Politics Today a Gidan Talabijin na Channels. Shirin N-Power wani shiri ne da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo da shi a ranar 8 ga watan Yunin 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi tsakanin matasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: