Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rabon Naira miliyan 950 ga dattawa marasa galihu guda 250

0 266

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da rabon Naira miliyan 950 ga wasu dattawa marasa galihu su 250 a fadin kasar nan.

A yayin da take kaddamar da shirin a Abuja, Oluremi ta ce kowace jiha za ta samu kudi Naira miliyan 25 yayin da kowace dattijuwa da aka zaba cikin wannan shiri zata samu kudi Naira dubu dari.

Uwargidan su gajiyar wannan tallafi ba tare da nuna wariya ba. Ta ce wannan shirin zai tallafawa mabukata 250 da tsofaffi masu shekaru 65 zuwa sama daga cikin jihohi 36 na kasar nan da babban birnin tarayya Abuja da kuma tsofaffin matan kungiyar  sojoji da ‘yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: