Gwamnatin tarayya ta dage kaddamar da shirin bayar da lamunin karatu na dalibai

0 102

Gwamnatin tarayya ta dage kaddamar da shirin bayar da lamunin karatu na dalibai da zai soma a yau Alhamis.

Sakataren zartarwa na Asusun Ba da Lamunin Ilimi Akintunde Sawyer shine ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a jiya Talata.

Sawyer ya ce an dage kaddamar da shirin ne saboda akwai wasu gyare-gyare da ake yi.

Sai dai bai bayyana sabuwar ranar kaddama da shirin na bayarda lamin karatun  ba. Tun da farko dai an tsara bayarda lamunin ne a watan Satumba, amma an jinkirta aiwatar da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: