Gwamnatin tarayya ta jajanta wa ’yan Najeriya kan wahalhalun da ake sha sakamakon karancin man fetur

0 109

Gwamnatin tarayya ta jajanta wa ’yan Najeriya kan wahalhalun da ake sha sakamakon karancin man fetur tare da yin kira da a yi hakuri wajen lalubo mafita mai dorewa dangane da matsalar.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ne ya yi wannan roko a jiya a wata sanarwa da babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa Horatius Egua ya fitar.

Ya kuma yabawa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) bisa nuna damuwa da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ta hanyar bayar da hakuri.

Ministan ya kuma ce ma’aikatan hukumar kula da harkokin man fetur sun fita kan tituna da gidajen mai domin ganin lamarin ya daidaita cikin gaggawa.

Timipre Sylva ya ce matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka ga dukkan bangarorin da hukumomin da abin ya shafa, shi ne su hada kai don ganin an shawo kan matsalar cikin gaggawa.

Ya kara da cewa al’ummar Najeriya sun cancanci rayuwa mai kyau kuma gwamnati ta kuduri aniyar dora kasar kan turbar wadatar albarkatun man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: