

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Watanni 8 bayan sace dalibai 80 da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, sama da 10 daga cikinsu na hannun wadanda suka yi garkuwa da su, duk da biyan kudin fansa da musayar fursunoni a lokuta daban-daban.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa akalla dalibai mata 13 ne aka aurar da su ga ‘yan bindiga kuma wasu daga cikinsu sun riga sun samu juna biyu.
A ranar 17 ga watan Yuni ne wasu ‘yan bindiga da ke biyayya ga wani shugabansu Dogo Gide.
Suka afkawa makarantar tare da sace dalibai da dama da Malamai biyar na makarantar mallakar gwamnatin tarayya.
Jaridar ta Daily Trust ta kuma rawaito cewa har yanzu Dogo Gide na rike da dalibai 11 zuwa 14 kuma 1 daga cikinsu namiji ne.
Har ila yau, wani malamin makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kaduna yana hannun wadanda suka yi garkuwa da shi, sama da watanni 7 bayan da wasu mahara suka kama shi tare da dalibansa da daddare.
Inda suka kashe jami’an tsaro biyu da ke gadi a makarantar.