Gwamnatin tarayya ta kaddamar da cibiyoyin iskar gas guda bakwai a fadin Najeriya

0 215

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin samar da motoci masu amfani da iskar gas, inda ta bude cibiyoyin iskar gas guda bakwai a fadin kasa.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya kaddamar da shirin a hukumance jiya a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

A yayin mika motocin bas din masu amfani da iskar gas ga fadar gwamnatin shugaban kasa, shugaban kwamitin gudanarwa na CNG na shugaban kasa, Zacch Adedeji, wanda ya samu wakilcin babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur (NMDPRA) Mista Farouk Ahmed, ya sanar da cewa gwamnati ta cire Haraji bai daya akan siyan motocin.

Adedeji ya ce manufar ita ce gina makoma mai dorewa, ta yadda za a yi amfani da tsaftataccen makamashi mai araha a Najeriya, wato iskar gas.

Ya kuma bayyana cewa ana kan shirye-shiryen gwamnati na samar da cibiyoyi da dama a fadin kasar nan cikin makonni biyu masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: