Gwamnatin tarayya ta koka kan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai
Gwamnatin tarayya ta koka kan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a jihar Sokoto, inda ta ce jarirai 44 cikin 100 da aka haifa a jihar ne ke mutuwa.
Don haka, ta nemi da a gaggauta samarda mafita akan mace-macen mata da jarirai a fadin jihar.
Mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman mai kula da kwamitin harkokin kiwon lafiya, Salma Ibrahim, ta bada wannan shawarar yayin ziyarar ban girma da ta kaiwa gwamna Ahmed Aliyu a jiya Alhamis.
Ta bayyana cewa har yanzu jihar Sokoto ce ke da mafi girman adadin mace-macen mata da jarirai a kasar nan.
Ta kuma lura da cewar akawai karuwar tsarin kayyade iyali a jihar, wanda ta ce zai rage mutuwar mata masu juna biyu.