Gwamnatin tarayya ta musanta sake dawo da tallafin man fetur, bayan da rahotanni suka bayyana cewa tana ware dimbim kudade wajen biyan dillalan mai don kauce wa tashin farashin.
Shugaban kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ne ya shaida wa manema labarai haka jim kadan bayan tattaunawarsa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
Ya kuma ce layuka da aka gani a gidajen mai a wasu sassan kasar sun samo asali ne daga matsalolin da aka samu wajen rarraba man daga kudanci zuwa arewacin kasar amma ba domin karancin sa ba.
Kyari ya ce babu wani batun tallafin mai, saboda an cire shi, kuma ba za a dawo da shi ba.
A cewar sa, akwai sama da Litar Mai Milyan 1.4 a teku da kuma cikin wanda aka tanada domin mutane Mele Kyari ya kuma tabbatarwa yan kasuwa cewa za’a bar farashin man fetur ya dai-daita kan sa domin yayi dai-dai da farashin kayan masarufi.