Gwamnatin Tarayya ta saki naira biliyan 50 domin biyan malaman jami’o’i a Najeriya

0 477

Gwamnatin Tarayya ta saki naira biliyan hamsin domin biyan hakkokin malaman jami’o’i da ma’aikatan da ba malamai ba a jami’o’in tarayya, kamar yadda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya alkawarta.

Ministan Ilimi, Dr Maruf Alausa ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wannan mataki alamar jajircewar shugaban ce wajen sauya fannin ilimi zuwa wani ginshiƙin ci gaban ƙasa.

A cewarsa, wannan tallafi ba kawai na kudi ba ne, illa matakin tabbatar da yadda shugaban ke daraja matasa da rawar da malamai ke takawa wajen gina su.

Alausa ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na godiya ga hadin kai da kwanciyar hankali a jami’o’i, wanda hakan ya haifar da zaman lafiya ba tare da yajin aiki ba, wanda yanzu ke zama tarihi a Najeriya, in ji shi.

Leave a Reply