Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Kungiyar Dake Taimakawa Yan Gudun Hijira

0 79

Gwamnatin Tarayya ta yabawa wata kungiyar kasa da kasa dake taimakawa yan gudun hijira bisa taimakawar da tayi wajen dawo da yan Najeriya da suka rasa matsugunni a kasashen waje zuwa gida da kuma bayar da tallafi ga marasa karfi a yankin Arewa Maso Gabas.

Cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar Mista Fadinan Nwoye ya fitar, Babban Sakataren Ma’aikatar kasashen waje, Ambassada Mustapha Sulaiman shine yayi wannan yabon yayin da yake karbar bakuncin tawagar kungiyar, karkashin jagorancin Mista Richard Danziga, daraktan kungiyar na Afirka Ta Yamma

Ambassada Mustapha Sulaiman ya yabawa kungiyar bisa kyawawan ayyukanta, inda ya nanata jajircewar gwamnati wajen cika alkawarun data daukarwa kungiyar.

Daga nan sai yayi kira ga kungiyar data banbance rabe-raben yan gudun hijira, da kuma tabbatar da samun ma’adanar bayanai, tare da assasa hanyoyin magance matsalar gudun hijira a kasar.

A nasa jawabin, Daraktan Kugiyar, Richard Danziga yace, tawagar sunje ma’aikatar ne domin bayyanawa Babban Sakataren irin ayyukan kungiyar wadanda suka hada da dawo da yan Najeriya da suka rasa matsugunni daga kasashen Turai da Libya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: