Maniyyata 32,402 Yan Najeriya Sun Isa Birnin Madina Domin Hajjin Bana

0 134

Hukumar Alhazai ta kasa tace ta kai maniyyata 32,402 zuwa Birnin Madina na kasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana.

Gabadaya Alhazan da suka fito daga kowane sashe na duniya, ake sa ran zasu bar Madinah zuwa Makkah ranar 7 ga watan Augustan da muke ciki, daga nan kuma sai su wuce Minnah domin fara ayyukan Hajji.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a madina, Hukumar Alhazan ta kasa tace tayi jigilar jirage 66, kuma a yau jirgi ya tashi daga jihar Kebbi zuwa Madina dauke da maniyyata 430.

Jagoran hukumar alhazan ta kasa a Madinah, Alhaji Ahmed Maigari, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, yace hukumar zata kai dukkannin maniyyata zuwa Saudiyya kafin ranar karshe. Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa Alhazan Najeriya dake Madinah suna cigaba da ayyukan ibada, kuma sun ziyarci guraren tarihi, kafin a kai su zuwa Birnin Makkah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: