

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Akalla yara yan makarantar firamare 27,960 ake ciyarwa a Karamar hukumar Gumel ta Jihar Jigawa karkashin shirin ciyar da dalibai yan makaranta na gwamnatin tarayya.
Jagoran shirin a yankin, Alhaji Ibrahim Nayaya, shine ya bayyana hakan a Gumel yayinda yake mika kwanuka da cokula guda 152 ga masu dafa abinci karkashin shirin.
A cewarsa ana shirin a makarantun firamare 57 dake yankin.
Alhaji Ibrahim Nayaya yace gwamnatin tarayya ce ta samar da kwanukan da cokulan bisa kokarin ganin an ciyar da daliban ta tsaftatacciyar hanya.
Jagoran sai ya umarci Shugabannin Makarantun Firamare dasu kai masa rahoton duk wata mai dafa abincin dake bawa daliban abinci a kwano mara tsafta, domin daukar mataki.
Da yake Magana a wajen rabon, Shugaban Karamar Hukumar Gumel, Alhaji Aminu Sani, ya yabawa gwamnati bisa ciyar da daliban kyauta, inda yace hakan ya haifar da karuwar yaran da ake sakawa a makaranta a yankin.