Nasara Ga PDP: Kotu Ta Umarci A Kawo Ainihin Sakamakon Zaben 23/03/2019

0 101

Shugabar kotun sauraren korafin zaben gwamnan jihar Kano, Mai Sharia Halima Shamaki, ta umarci rundunar yansandan kasa dasu mikawa kotun sakamakon zaben gwamnan daya gabata na ranar 23 ga watan Maris.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa ya rawaito cewa dan takarar jam’iyyar PDP yayin zaben Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa suna kalubalantar ayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

Mai sharia Halima Shamaki ta umarci Kwamishinan yansandan na jihar ta Kano, Mista Ahmed Iliyasu, da ya fito da takardun da masu kara suka nema, ranar 5 ga watan Augustan da muke ciki.

Tunda farko, lauyan masu kara, Adegboyega Awomolo, ya bukaci kotun data umarci kwamishinan yansandan daya bawa jam’iyyar PDP takardun sakamakon zaben da aka bawa yansanda.

Hakazalika, jami’in dansandan dake kula da bangaren shariah, SP Sunday Ekwe, yace rundunar da karbi sammacin kotu ranar 30 ga watan Yuli da misalin karfe 4:45 na yamma, tana bukatar kwamishinan yansanda daya bayar da takardun sakamakon zaben da akayi amfani dasu lokacin zaben gwamnan daya gabata.

Sai ya nemi kotun data bashi lokaci domin komawa ofishin yansanda domin bincikawa ko suna da wadannan takardun.

Daga nan mai sharia Halima Shamaki ta dage sauraron shariar zuwa yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: