Bauchi Tayi Damarar Magance Kwararowar Hamada

0 120

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya kaddamar da shirin shuka bishiyoyi na shekarar 2019, mai taken ‘a dasa bisa dan ceto muhalli’

Gwamnan ya kaddamar da shirin ne a garin Gadau dake jihar ta Bauchi, inda ya nuna takaicin yadda jihar ke fuskantar kalubalen muhalli daban daban irinsu fari, kwararowar hamada, zaizayar kasa da kuma ambaliyar ruwa.

Yace sakamakon matsalolin na muhalli sun haifar da asarar gonakin noma, inda ya kara da cewa hakan ya shafi zamntakewar mutane da yau da kullum.

Daga nan sai yayi kira da za a lalubo hanyar magance kalubalen muhalli ta hanyar dashen bishioyi domin dakile matsalar.

Gwamna Bala Muhammad yace shirin na dashen bishiyoyi na wannan shekara ba a iya dashen zai tsaya ba, zai hada da wayar da kan jama’a, samarda tare da rabbawa iri a ko’ina a fadin jiha, tare da kare dazukan da ake da su.

Ya kara da cewa shirin na dashen bishiya daga yanzu zai cigaba da dorewa, kasancewar gwamnati zata cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da wadatar dukkan abubuwan da ake bukata wajen shirin.

Daga nan Gwamnan sai ya umarci shugabannin kananan hukumomi 20 dake jihar da suyi koyi da aiki a kananan hukumominsu.

Tunda farko, Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Muhalli ta jihar, Alhaji Ahmed Zalanga, ya bayyana gangamin wayar da kan da ake gudanarwa duk shekara, anayi ne da zummar wayar da kan jama’a akan muhimmancin shirin dashen bishiyoyi a matsayin maganin tarin kalubalen dake fuskantar muhalli a kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: