Ga Mari Ga Tsinka Jaka: Mazauna Takur A Dutse Sunyi Zanga-Zanga Kan Tsada Da Yawan Dauke Wutar Lantarki

0 128

Mazauna Unguwar Takur a Birnin Dutse, sun bazama zuwa ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Shiyyar Kano (KEDCO), na yankin Dutse, domin zanga-zanga akan yawaitar dauke wutar lantarki da kuma neman su biya kudade masu yawa a matsayin kudin wuta.

Wanda ya jagoranci Zanga-Zangar zuwa ofishin KEDCO na Yankin Dutse, Mallam Yusuf Da-Sanin-Allah, ya nuna takaicin yadda ake cajarsu kudade masu yawa na wutar lantarkin da suka yi amfani da ita, alhalin suna fuskantar daukewar wutar lantarkin akai-akai.

Yusuf Da-Sanin-Allah, wanda yayi jawabi a madadin masu zanga-zangar, yayi zargin cewa kamfanin na KEDCO yana cajar kowane gida a unguwar kudade tsakanin Naira 8,000 zuwa Naira 10,000 kowane wata, koda ba’a samu wadatacciyar wutar lantarki ba.

A cewarsa, duk lokacin da jama’a suka yi korafi ko suka nemi bayani daga ma’aikatan KEDCO, ma’aikatan zasu yi musu barazanar yanke musu wutar lantarki.

Da aka nemi jin ta bakin Manajan KEDCO na Yankin Dutse, Mallam Sai’du Sambo, sai yace ba zaiyi Magana da yan jarida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: