Gwamnatin Tarayya Tayi Allah Wadai da Kisan da Akayi a Adamawa

0 165

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun far wa wani ƙauye a jihar Adamawa, inda suka kashe mutum uku tare da lalata kayayyaki da dama.
Mazauna ƙauyen na Dabna da ke karamar hukumar Hong na jihar ne sun ce mayaƙan sun shigo ƙauyen ne kan babura a safiyar ranar Litinin, inda suka yi ta harba bindigogi kan mai uwa da wabi tare da sace kayan abinci da kuma magunguna.
Wani jami’in bijilanti ya ce fararen hula huɗu ne suka mutu a harin, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin maharan ya rasa ransa yayin artabu da wasu jami’ansu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje ya fitar, rundunar sun tabbatar da kai harin, inda suka yi Allah-wadai da shi.
Ya ce ya zuwa yanzu sun tura tawaga zuwa yankin domin kwantar da hankula.
A watan Yulin 2021, wasu da ake zargin ƴan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram suka kaddamar da hari a ƙauyen Dabna tare da kashe mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: