Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki kan hauhawar farashin kayan abinci

0 228

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kare hakkin mai saye da sayarwa ta Tarayya, za ta fara sanya takunkumi ga mambobin kungiyoyin kasuwanci da ke da alaka da cin hanci da rashawa, tashin gwauron zabi kan farashin abinci.

Babban jami’in hukumar Babatunde Irukera shi ne ya bayyana haka a jiya a yayin wani taron tattaunawa da hukumar ta shirya domin tattaunawa kan farashin kayan abinci.

A cewar Irukera, wasu kungiyoyin yan kasuwa sun kafa wasu hanyoyi domin shiga ayyukan da ba su dace ba wanda ya kai ga haifar da tashin kayan abinci na yau da kullun. Ya yi nuni da cewa daukar tsauraran matakai kan hauhawar farashin kayan abinci ya zama wajibi bisa la’akari da ayyana dokar ta baci kan samar da abinci da shugaban kasar ya yi a matsayin matakin gaggawa a makon jiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: