Gwamnatin tarayya za ta kara samar da kudade ga fannin kiwon lafiya a Najeriya

0 75

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta kara samar da kudade ga fannin kiwon lafiya ta hanyar asusun samar da kiwon lafiya da sauran tsare-tsare.

Ya bayyana haka ne jiya a lokacin da ya karbi bakuncin babbar tawagar kungiyar Gavi a Najeriya, karkashin jagorancin babban jami’in gudanarwa, Dr Seth Berkley, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar, ya ce ana samun cigaba wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba a dabarun rigakafi da inganta tsarin kiwon lafiya a matakin farko na Najeriya.

Ya ce rahotannin farko sun nuna cewa amfani da allurar rigakafin yara ya karu daga kashi 33 cikin 100 a shekarar 2017 zuwa kashi 63 cikin 100 a shekarar 2019.

Shugaba Buhari ya yaba da amincewar kungiyar Gavi na tsawaita wa’adin aiki a Najeriya daga shekarar 2022 zuwa 2028, da kuma alkawarin hadin gwiwa wajen samar da kudi sama da dala biliyan 3 don sayan alluran rigakafi da inganta tsarin kiwon lafiya a fadin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: