Gwamnatin Najeriya na kara fadada ayyukan hako mai domin cin gajiyar tashin farashin danyen mai a duniya

0 69

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya ce Gwamnatin Tarayya na kara fadada ayyukan hako mai domin cin gajiyar tashin farashin danyen mai a duniya.

Timipre Sylva ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai kan taron makamashi na kasa da kasa na Najeriya da zai gudana daga ranar 27 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga watan Maris.

Ministan na mayar da martani ne game da farashin danyen mai a duniya wanda yayi tashin gwauron zabi zuwa dala 103.33 kan kowacce ganga saboda rikici tsakanin Rasha da Ukraine.

Farashin danyen man ya tashi saboda damuwar da ke tattare da karancinsa a duniya sakamakon tasirin takunkumin cinikayya kan kasar Rasha, jigo a samar da danyen mai a duniya, bayan ta mamaye kasar Ukraine.

Da yake mayar da martani kan hauhawar farashin danyen man da ya tashi zuwa dala 103.33 daga dala 96 kan kowacce ganga a kasuwannin duniya, ministan yace dole Najeriya ta kara yawan man da take hakowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: