Mun damu kan rikicin Rasha da Ukraine kuma muna yin kira da a wanzar da zaman lafiya domin warware rikicin – Gwamnatin Najeriya

0 30

Gwamnatin tarayya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya, inda suka nuna damuwarsu kan rikicin Rasha da Ukraine tare da yin kira da a wanzar da zaman lafiya domin warware rikicin.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ya gana da wakilan jiya a Abuja, inda ya ce gwamnatin tarayya ta yi kira da a samar da zaman lafiya tare da yin amfani da diflomasiyya wajen warware duk wata matsala.

Geoffrey Onyeama ya ce Najeriya ba ta amince da matakin wuce gona da iri na Rasha ba, yana mai kira ga Rasha da ta janye dakarunta.

Da take zantawa da manema labarai bayan taron na sirri, Jakadiyar Jamus a Najeriya, Birgitt Ory, wadda kuma ita ce shugabar kungiyar G7, ta yabawa kungiyar Tarayyar Afirka (AU) bisa furucin da ta yi kan halin da ake ciki.

Birgitt Ory, wadda ita ma ta yabawa Najeriyar bisa tsoma baki, ta ce Najeriya babbar murya ce da duniya ke bukatar ji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: