Gwanatin Tarayya ta himmatu wajen inganta karfin sashen Fetur da Gas

0 138

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan abubuwan cikin gida, Sanata Joel Onowakpo Thomas, ya sake tabbatar da kudurin Shugaban kasa Bola Tinubu na bunkasa karfin sashin fetur da iskar gas na cikin gida da sauran bangarorin a matsayin tabbataccen hanyar samar da ayyukan yi.

Ya yi wannan jawabi ne bayan ziyarar sa ido kan cibiyoyi da wuraren ayyukan hukumar bunkasa abun ciki ta Nijeriya (NCDMB) a Jihar Bayelsa.

Ya ce domin cimma wannan nasarar, akwai bukatar kara kyautata aikin hadin guiwa a tsakanin kwamitin majalisar da kuma hukumar NCDMB domin tabbatar da dokokin da suke akwai ana amfani da su yadda ya kamata. Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010.

Leave a Reply