Hukumar yanayi ta ƙasa, NiMet, ta fitar da hasashen cewa daga Asabar zuwa Litinin, za a fuskanci guguwar iska da ruwan sama a sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da arewacin Taraba, Kebbi, Zamfara, Kaduna da Adamawa, inda aka sa ran za a yi ruwan sama da hadari da safe da kuma daga baya a rana a jihohin Gombe, Sokoto, Bauchi da Borno.
A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, jihohin Benue, Filato, Neja, Nasarawa da Abuja za su fuskanci guguwar hadari da ruwan sama da safe da kuma daga baya a yamma, yayin da kudu za ta kasance da gizagizai da damina a sassa kamar Enugu, Legas, Bayelsa da Cross River.
Hasashen ya ci gaba har zuwa Litinin inda NiMet ta yi gargadi kan yiwuwar guguwar iska kafin ruwan sama a jihohin Kebbi, Kano, Katsina da Bauchi, inda aka bukaci jama’a su matse abubuwan da iska ke iya tafka illa da kuma kada su yi tuƙi a lokacin hadari. Hukumar ta kuma gargadi kamfanonin jiragen sama da su riƙa karɓar bayanan yanayi na filin jirgi kafin tashi, tare da shawarwarin kariya ga jama’a da suka haɗa da cire na’urorin lantarki daga socket da kuma gujewa tsayawa a ƙarƙashin bishiyu a lokacin hadari.