Shugaban Hukumar, Malam Jalal Arabi ya ce ana bukatar maniyyatan da suka fito daga yankin Kudancin Najeriya su biya miliyan 4 da dubu 899 a matsayin kudin aikin Hajji, yayin da wadanda ke yankin Arewa za su biya miliyan 4 da dubu 699.
Hakama yace wadanda suka fito daga Yola da Maiduguri za su biya miliyan 4 da dubu 679.
Mataimakiyar daraktan hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta bayyana yadda tun da farko shugaban hukumar ta NAHCON ya kudiri aniyar daidaita farashin kudin aikin Hajjin bana akan Naira miliyan 4 da rabi
Hukumar NAHCON ta tabbatar wa al’umma cewa ta himmatu wajen ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara da kuma kaucewa duk wani kalubalen da ke tattare da canjin kudaden kasashen waje. Hukumar ta yaba da fahimta da hadin kan al’ummar Musulmin Najeriya.