Zanga-zanga ta barke a yankin Rigachikum biyo bayan kashe wani dan kasuwa da jami’in tsaro yayi

0 123

Bayanai daga yankin Rigachikum a karamar hakumar Igabi dake jihar Kaduna sun bayyana yada mazauna yankin a jiya suka soma zanga-zanga nuna rashin amincewa bayan zargin wani jami’in tsaro da kashe wani dan kasuwa.

Manema labarai sun tattaro cewa wanda lamarin ya shafa ya mutu ne sanadin harbin bindiga lokacin da yake kokarin rufe shagonsa, bayan wasu yan barandar siyasa a yankin sun yi kokarin mamaye wata rumfar zabe a ranar asabat.

Mahaifiyar wanda lamarin ya faru akan sa Zulai Abdullahi da matar sa Safiya Usman sun bukaci hakumomi suyi duk mai yiyuwa domin tabbatar da anyi masa adalci.

Kakakin yansandan jihar Kaduna ASP Mansur Hassan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace kwamashinan yansandan jihar Audu Ali Dabigi, ya bayar umarnin soma binciken gaggawa kan lamarin. Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Igabi a tarayya Hussaini Muhammad Jallo ya bukaci rundunar yan sanda ta tabbatarda nemo makashin Mansur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: