Hukumar Asusun Adashen Gata na fansho na jihar Jigawa ta biya fiye da miliyan 39,453 a matsayin hakkokin ma’aikata

0 72

Hukumar Asusun Adashen Gata na Fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa tace ta biya kudi fiye da naira miliyan dubu talatin da tara da miliyan dari hudu da hamsin da uku a matsayin hakkokin maaikata da kuma kudaden fansho na wata wata a tsakanin watan Mayu na 2015 zuwa wannan watan.

Sakataren zartarwa na asusun Alhaji Kamilu Aliyu Musa ya sanar da hakan a lokacin da tawagar shugaban kungiyar maaikatan kananan hukumomi na kasa Comrade Ambali Akeem Olatunji suka ziyarci asusun..

Yace daga adadin kudaden sun biya naira miliyan dubu goma sha hudu da miliyan dari biyu da hamsin da shida a matsayin hakkokin maaikata da kuma naira miliyan dubu ashirin da biyar da miliyan dari da casein da shida a matsayin kudaden fansho na wata wata a wadannan shekaru.

Alhaji Kamilu Aliyu Musa kuma Durbin Babura yace maaikatan jiha da kananan hukumomi dana sashen ilmi 8,474 ne suka samu hakkokin nasu.

Yayinda asusun yake da yan fansho na jiha da kananan hukumomi dana sashen ilmi 12,868.

Ya taallaka nasarorin da asusun ke samu akan hadin kai da goyan bayan gwamna Muhammad Badaru Abubakar.

A nasa jawabin shugaban kungiyar NULGE na kasa Comrade Ambali Hakeem ya nuna gamsuwa da irin aiyukan asusun wanda a cewar sa jihar jigawa tana kan gaba wajen biyan hakkokin maaikata..

Inda kuma ya bukaci sauran jihohi da su koyi tsarin jigawa wajen biyan hakkon maaikatan jiha da kananan Hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: