Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta bayyana rashin jin dadin ta game da gurbataccen man fetur da aka baiwa ‘yan Najeriya tare da yin kira da a gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a karshen taronta a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa a jiya Litinin.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Okezie Ikpeazu (Abia); Ahmadu Fintiri (Adamawa); Udom Emmanuel (Akwa Ibom); Bala Mohammed (Bauchi); Douye Diri (Bayelsa); Samuel Ortom (Benue); Ifeanyi Okowa (Delta); Godwin Obaseki (Edo); Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Oluseyi Makinde (Oyo) da kuma Nyesom Wike (Rivers).

Ikpeazu, mataimakin shugaban kungiyyar, wanda ya karanta sanarwar ga manema labarai, ya ce yadda gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ke tafiyar da tsarin tallafin man fetur ya cika da rashin gaskiya.

Ya kuma bayyana cewa alkaluman cin abinci da gwamnati ta kama da alama karya ne da wuce gona da iri.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: