Hukumar JAMB ta sake tsawaita lokacin rajistar neman gurbin karatu na (D.E) shekarar 2024

0 343

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta sake tsawaita lokacin rajistar neman gurbin karatu na (D.E) shekarar 2024.

A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na X, Hukumar ta sanar da cewa masu neman shiga jarabawar an kara tsawaita rajistar da zuwa makonni biyu.

Da wannan cigaban da aka samu yanzu ranar rufewa rijistar ita ce 25 ga Afrilu, 2024. Hukumar JAMB ta fara tsawaita wa’adin zuwa ranar 11 ga watan Afrilu daga ranar 28 ga watan Maris, domin baiwa dukkanin masu neman yin rajistar, sakamakon wasu kalubalen da aka fuskanta a matakin tantance wadanda za su rubuta jarabawar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: