Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta jinjinawa Gwamna Mallam Umar Namadi

0 163

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta jinjinawa Gwamna Mallam Umar Namadi bisa baiwa hukumar rancen Naira Miliyan Dubu Biyu da Miliyan Dari Biyu da Hamsin domin tanadin kujerun aikin hajjin bana ga maniyata.

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan yabo.

Yace wannan shine karon farko da wani gwamna a kasar nan ya baiwa hukumar alhazai rancen kudi domin sayen kujerun aikin hajji

Alhaji Ahmed Umar Labbo yace wannan karamci ne da gwamnan ya yiwa hukumar alhazai da maniyata da kuma sauran alummar musulmi. Ya kara da cewar hatta shugaban hukumar aikin hajji ta kasa ya godewa Gwamnan bisa wannan karamci da ya yiwa hukumar da kuma kasa baki daya

Leave a Reply

%d bloggers like this: